Dubun Wani Mai Gadin Kamfanin Takalma Ta Cika Kan Zargin Satar Miliyoyin Kudi A kano

Mai Gadi

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar kwato wasu miliyoyin kudi daga wajen wani mai gadin kamfanin Takalma na Asia Plastic dake unguwar Jogana a karamar hukumar Gezawa dake jahar.

AlfijirLabarai ta ruwaito an kama wanda ake zargin mai suna ย Sadam Habu, dan asalin jahar Adamawa, inda ya fasa ofishin mai biyan kudi, bayan ya saci miliyoyin naira a cikin Akwati sannan ya bankawa ofishin wuta.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano , SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu labarin faruwar lamarin a ranar 28 ga watan Augustan 2024, inda suka yi nasarar cafke wanda ake zargin a lokacin da yake yunkurin tserewa da kudin.

Bayanai sun bayyana cewa kudin da aka samu a cikin akwatin da ya zuba kudin sun haura naira miliyan 20, kuma yanzu haka rundunar ta na ci gaba da gudanar da bincike wanda da zarar an kammala za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan๐Ÿ‘‡

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *