Muzambilu Ado, Darakta mai rikon mukamin Sashen Hulda da ‘Yan Jaridu da Kididdiga a Kotun Daukaka Kara ta Shari’a ta Jihar Kano, ya shigar da kara a kotun Kwadago ta Kasa, ya na neman diyyar Naira Milyan 100 tare da neman rusa tilasta shi da hukumar ta yi na tafiya ritayar dole.
Hukumar Kula da Da’ar Maaikatan Shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta umarci Muzambilu Ado da ya tafi ritayar dole saboda zargin rashin daidaito, sauya bayanan karatunsa da kuma yin amfani da takardun shaidar karatu na bogi don samun aiki a Hukumar Shari’a ta Jihar Kano.
Ado ya bayyana cewar wannan umarni ya bata masa suna kuma ya lalata masa aikin da ya gina tsawon shekaru.
Hukumar JSC ta Jihar Kano, cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 6 ga Yuli, 2026 da mai magana da yawunta Baba Jibo Ibrahim ya fitar, ta bayyana cewa an gano rashin daidaito da sauya bayanai a takardun karatunsa, kuma ta umarce shi da ya yi ritayar dole domin zama izina ga sauran ma’aikata.
Sanarwar ta ce:
Hukumar JSC ta umarci Muzambilu Ado, Darakta mai rikon Sashen ‘Yan Jaridu da Kididdiga a Kotun Daukaka Kara ta Shari’a, da ya tafi ritayar dole nan take bayan kwamitin tantancewa ya gano manyan matsaloli a takardun karatunsa, ciki har da sauya bayanai da kuma samun shiga Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Kasa ba tare da amincewar Hukumar ba.
Sai dai a cikin karar da ya shigar, Ado ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa na sauya bayanai da rashin daidaito a takardun karatunsa. Yace bita da kulli aka
Ya bayyana cewa an dauke shi aiki a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano tun 2006 da Diploma a Katatun Nazarin Mulki daga Makarantar Fasaha KadPoly Kaduna yana mai jaddada cewa bai taba gabatar da takardar HND a matsayin cancantarsa ba a duk wani tantancewa da ya halarta.
Ya ce wannan ya saba da ikirarin JSC cewa ya yi jabu da takardar HND tare da sauya maki.
Game Digiri a Katatun Lauya (LLB) Muzambilu Ado ya bayyana cewa ya yi rajista a Jami’ar Imperial dake Sudan, inda ya samu Shaidar Digiri LLB a shekarar 2022.
Haka kuma, bisa ga amsar da Jami’ar Imperial ta aika wa Sakatariyar JSC Kano game da bukatar tantance takardun karatun Muzambilu Ado, makarantar ta tabbatar da cewa ya yi rajista daidai kuma ya kammala dukkan darussa da ake bukata.
Jami’ar ta kara da cewa Ado ya fara karatun Digiri a Shari’a a Jami’ar Alnahda dake Jamhuriyar Nijar. Daga baya ya nemi sauyi zuwa Jami’ar Imperial domin yin karatun gajeren zango, bayan Alnahda ta kasa mika sunansa ga makarantar koyon aikin Lauya ta Kasa
saboda rashin samun sahihanci daga makarantar.
Ya musanta ikirarin cewa JSC ta yi la’akari ne da korafin da wani Sani Manzo ya rubuta inda ya bayyana suna a matsayin sunan bogi da aka kirkira a fake a cutar da wani
Ya kuma ce bai taba samun kwafin koke akan korafin da aka yi akan saba, don kare kansa, kuma ba a taba aika masa da tambaya ba, wanda ya ce yin hakan ya saba ka’idojin aikin gwamnati.
Game da bukatarsa ta shiga Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Kasa, Muzambilu ya ce su biyar ne suka nema, amma sauran hudu aka amince da su, yayin da shi ba a aika masa da sanarwa ba.
Ya bayyana cewa bayan ya mika bukatarsa, abin da ake sa ran shi ne ko dai amincewa ko kin amincewa, amma bai samu ko daya ba.
Ya kara da cewa bayan ya ci gaba da shirin, sai aka zarge shi da laifi na samun tafiya kataru ba tare da izini ba.
Ya roki kotu ta soke hukuncin da Makarantar Koyon Aikin Lauya ta yi na korar sa, yana mai cewa rashin iya tuntubar Jami’ar Imperial ta hanyar adireshin imel na hukuma ba laifinsa ba ne.
Ya yi ikirarin cewa Makarantar ya kamata ta mallaki hanyoyi da dama na tantance takardun karatun dalibai, ba wai ta takaita kanta ga amfani da adireshin imel na ofis kadai ba.
Saboda haka ya roki kotu ta bayyana umarnin da JSC ta ba shi a matsayin maras inganci, yana mai cewa bai yi daidai da doka ba.
Da aka tuntubi Baba Jibo Ibrahim, mai magana da yawun Ma’aikatar Shari’a ta Kano, ya ki yin tsokaci kai tsaye kan zarge-zargen da Muzambilu Ado ya gabatar.
Ya bayyana cewa bai dace ya shiga muhawara da Ado ba bayan an umarce shi da ya yi murabus daga aiki, kuma saboda al’amarin yana gaban kotu.
Sai dai ya ce, a maslaha ta jama’a, yana da muhimmanci a fayyace bayanan da Ado ya yada.
A cewar Jibo, matsalar ta samo asali ne daga koke da wani ma’aikacin shari’a a Kotun Daukaka Kara ta Shari’a Kano, Sani Manzo, ya gabatar ga JSC, sannan ita Kuma JSC ta sanar da Ma’aikatar Koyon Aikin Lauya don tantancewa.
“Koken ya zargi rashin daidaito a takardun karatun Muzambilu Ado kuma ya bukaci tantancewa.”
Mai magana da yawun ya jaddada cewa Manzo ba sunan bogi ba ne.
Makarantar, bayan ta karbi koken, ta aika da wasika zuwa Jami’ar Imperial ta amfani da adireshin imel da ke cikin sakamakon da mai karar ya gabatar.
Sai dai dukkan imel din sun dawo ba a isar ba.
Da aka tambayi Baba Jibo don fayyace amsar da ake ikirarin ta fito daga Jami’ar Imperial Sudan, zuwa JSC Kano, ya bayyana cewa mai karar na iya yin jabu da takardar, domin bai gabatar da ita ba lokacin da kwamitin ya kira shi.
Game da shigar Ado zuwa Makarantar Koyon Aikin Lauya Ta Kasa, mai magana da yawun ya jaddada cewa bai kamata ya ci gaba da karatu ba tare da izini ba.
Ya kara da cewa yin watsi da zarge-zargen ba zai halatta ci gaba da karatu ba tare da izini ba.
Baba Jibo ya kara da cewa a cikin wata wasika daga Makarantar Koyon Aikin Lauya zuwa Hukumar JSC Kano, Makarantar ta soke lasisin mai karar na ci gaba da karatu bayan ya kasa bayar da isasshen bayani game da takardun karatunsa.
Ya ce:
“Makarantar Koyon Aikin Lauya ta yi kokarin tantance takardun karatunsa ta hanyar tuntubar Jami’ar Imperial ta adireshin imel na hukuma. Sai dai dukkan imel din sun dawo ba a isar ba, kuma ba a samu amsa ba, wanda hanka yake nuna rashin inganci na takardun”
Da aka tambaye shi kan takardun karatun mai karar a lokacin daukar aiki, Baba Jibo ya bayyana cewa matsalar ba kan takardun da ya gabatar ba ce, sai dai rashin daidaito da aka gano a cikinsu, wanda hakan ya shafi mutuncinsa a matsayin ma’aikacin shari’a.
Ya tabbatar da cewa JSC ta shirya kare matsayinta da hujjoji na gaskiya.
Justice Watch Hausa ta gano cewa yayin da Muzambilu Ado ke matsayin mai karar a shari’ar, wadanda ake karar sun hada da: Hukumar JSC ta Jihar Kano, Gwamnan Jihar Kano da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano.
Justice Watch Hausa
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
