“Ina tabbatar muku da cewa Gwamnatin Kano ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajan kawo karshen wannan ta’asa ta awon igiya”
Gwamnan na jihar Kano Wanda Kwamishinan Public Procurement Hon. Nura Iro Maaji ya wakilta ya bayyana cewa Gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf ya samar da filayen ne masu tsari da ababen more rayuwa da Tsaro da ma sauran abubuwan da zasu inganta rayuwar mazauna filayen da iyalansu.
Hon. Nura Iro Maaji Sumaila ya shawarci wadanda suka amfana da tsarin su yi amfani da su wajen cigaban rayuwarsu da ta iyalansu
A nasa jawabin Kwamishinan ma’aikatar kasa da tsare tsare ta jihar Kano Alh. Abduljabar Muhammad Umar ya bayyana cewa Fiye da mutane 2500 ne suka amfana da Shirin bada kyautar filayen da suka Hadar da Masu baiwa Gwamnan jihar Kano Alh.Abba Kabir Yusuf Sahawara Fiye da 400 da kuma Yan Dangwalen kuria na kananan Hukumomin 44 har su 1589.
Kwamishina Abduljabbar ya bukaci wadanda suka amfana da su yi kokarin raya filayen ta hanyar ginawa Maimakon sayarwa, domin inganta rayuwarsu da ta iyalinsu.
Hakazalika kwamishinan ya gargadi barayin kasa da ma masu awon igiya na jihar Kano cewar ma’aikatar Æ™asa ba za ta lamunci duk Wani nauin karya dokar Ma’aikatar ba, inda ya sha alwashin daukar matakin doka akan duk wanda hukumar ta kama da aikata laifi.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
