Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa Donald Trump ya yi musayar jiragen sama a asirce yayin da yake barin taron ƙungiyar tsaro ta NATO a Turkiyya a watan da ya gabata, a matsayin matakin kariya ga barazanar da zai iya fuskanta daga Iran.
Shugaban Amurka ya hau jirgin Air Force One a bainar jama’a kafin a yi a shigar da shi cikin wata babbar akwatin abinci a filin jirgin sama sannan a saka shi a jirgin sama na soja, ba tare da ‘yan jarida da wasu ma’aikatan Fadar White House sun sani ba, inji jaridar Washington Post.
Jami’ai sun shaida wa abokiyar hulɗar BBC ta Amurka CBS News cewa Amurka ta gano wata barazana ta gaskiya da Iran ke yi na harba makami mai linzami a kan jirgin. Fadar White House ba ta tabbatar da wannan sirrin ba.
A baya Trump ya ce shi ne “babban abin da Iran ke nema” a taron ƙolin da aka gudanar a Ankara.
Wannan matakin na sirri ya zo ne kwana guda bayan da Amurka ta sake sabunta hare-haren soji kan Iran bayan wargajewar tattaunawar da aka yi tsakanin Washington da Tehran don kawo ƙarshen yakin.
Trump ya isa Turkiyya a cikin sabon jirgin Boeing 747-8 da Qatar ta ba shi, amma ya sanar da cewa zai tafi da tsohon jirgin Air Force One ” bisa tsari”.
A ranar 8 ga Yuli, an nuna shi yana shiga jirgin saman shugaban ƙasar a filin jirgin saman Ankara.
Amma a cewar jaridar Washington Post, an kai shi a asirce zuwa wani ƙaramin jirgin sama na soja na C-32A – wani jirgin Boeing 757 da mataimakin shugaban ƙasa ke amfani da shi akai-akai – ta hanyar sunduƙin abinci da aka ɗaga zuwa matakin jirgin sama a gefe guda da inda ya hau.
Sawaba
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
