Kotun Majistare mai lamba 47 da ke Unguwar Zungeru a Jihar Kano, ta tura mutane biyu gidan yari bisa zargin haɗa baki wajen rushe wata gada da kwashe kayan cikinta a yankin Danjirima, da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso.
Jami’an Hukumar DSS ne suka gurfanar da mutanen, Danlami Sulaiman, wanda aka fi sani da Layayu, da Abdullahi Ibrahim, wanda aka fi sani da Maraki, bisa zargin haɗa baki, sata, keta, da kuma shiga wuri ba tare da izini ba.
Ana zargin mutanen biyu da zuwa gadar a ranar 22 ga watan Yuli, inda suka rushe ta tare da kwashe rodi da ƙarfen da ke cikinta, sannan suka yanka wasu filaye a wajen gadar.
A yayin zaman kotun, magatakardar kotun, Anas Zage, ya karanta wa wadanda ake zargin tuhume-tuhumen da ake yi musu, sai dai mutanen biyu sun musanta aikata laifukan.
Bayan sauraron bayanan, Mai Shari’a Abba Maiwada Abubakar ya bayar da umarnin a tura mutanen biyu gidan yari.
Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Satumbar 2026.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
