Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da wasu gine-gine tare da rufe wasu da ta ce an gina su ba bisa ƙa’ida ba a sassa daban-daban na birnin Kano.
Mai ɗaukar wa gwamnan Kano rahoto, Nanu Kankarofi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 17 ga Agusta, 2026.
Sanarwar ta ce tawagar kwamitin yaƙi da gine-ginen da ba bisa ƙa’ida ba, ƙarƙashin jagorancin Shugaban KANGIS, Ɗalhatu Aliyu Sani, ce ta gudanar da aikin.
An ce wasu daga cikin gine-ginen da aka dakatar ko rufe suna kusa da magudanan ruwa, inda gwamnatin ta ce matakin na da nufin tabbatar da bin dokokin amfani da filaye, kare wuraren jama’a da kuma magudanan ruwa a jihar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
