Gwamnatin Kano ta gargadi masu yin karin ruwa da ƙarin jini a Chemists na faɗin jihar.

FB IMG 1778588658214

Hukumar kula da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ta Jihar Kano (PHIMA) ce ta bayar da umarnin, inda ta ce shagunan sayar da magunguna ba su da izinin gudanar da ayyukan asibiti kamar karin ruwa da ƙarin jini.

Jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar Fauziyya Habib Mahmoud, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar.

Mukaddashiyar Sakatariyar zartarwa ta PHIMA, Hajiya Khadijah Hussein Sa’id, ta ce matakin ya yi daidai da manufar Gwamnatin Jihar Kano ta ba da fifiko wajen kare lafiyar al’umma, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran Yusuf.

Ta kara da cewar hukumar za ta ɗauki tsauraran matakai kan duk wani Chemist ko cibiyar lafiya da aka samu tana gudanar da irin waɗannan ayyuka ba tare da izinin doka ba, dai-dai da matakan da doka ta tanada.

Hukumar ta gargadi masu gudanar da irin waɗannan ayyuka da su daina nan take, tana mai cewa ba za ta yi sassauci ga duk wanda ya saɓa wa ƙa’idojin da aka gindaya domin kare lafiyar jama’a ba.

PHIMA ta kuma yi kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani “Chemist” ko wurin da ake gudanar da karin ruwa ko ƙarin jini ba bisa ƙa’ida ba zuwa ofishinta da ke Magaji Rumfa. Ta buƙaci masu gabatar da ƙorafe-ƙorafen su samar da hujjoji idan akwai, kamar hotuna, rasit ko wasu shaidu da ke tabbatar da gudanar da ayyukan.

An bayyana wannan matsaya ne yayin wani taron horaswa da PHIMA ta shirya wa masu cibiyoyin lafiya masu zaman kansu da Daraktocin Lafiya (Medical Directors), wanda ya mayar da hankali kan rubutawa da adana bayanan ayyukan lafiya bisa sahihan bayanai.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *