kwamitin kar ta kwana mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi karkashin Barrister Muhyi Magaji Rimin Gado ya sami nasarar damke wata mota cike da miyagun kwayoyi, ana kokarin shigar da su cikin jama’a a unguwar Bajallabe dake Kano.
Tun da fari dai ‘yan kwamitin unguwar Bajallabe ne suka ankare da motar daga bisani suka shaidawa kwamitin na kar ta kwana, wanda daga bisani jami’an kwamaitin karkashin CSP Bashir Gwadabe O/C Anti Daba suka yiwa yankin tsinke.
yanzu haka an mika wannan mota cajin ofis din Rijiyar Zaki, domin kammala tattara bayanai da daukar mataki na gaba.
Barrister Muhyi Magaji ya kuma jinjinawa yan kwamitin unguwar Bajallabe bisa yadda suka gabatar da wanann aiki cikin nutsuwa a jajircewa har ta kai an kai ga wannan nasara.
Kwamitin na kar ta kwana karkashin Muhyi Magaji na kara yin kira ga al’umma da su cigaba da sanya idanu a yankunan su da kuma sanar da kwamitin kan duk wani motsi da basu yadda da shi ba.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan ๐
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ๐๐
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
