Shekaru 50: Gwamnatin Kano za ta fara aikin sake yi wa filayen Jami’ar Bayero musamman Bangaren Rimin Zakara Iyaka

IMG 171932 03926 1788452383549

Gwamnatin Jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara aikin sake yi wa filayen Jami’ar Bayero ta Kano iyaka, musamman wuraren da rikicin filaye tsakanin jami’ar da al’ummar Rimin Zakara ya shafa, wanda ya kwashe kusan shekaru 50 ana ɗauki ba daɗi.

 

Hakan ya biyo bayan kammala shirye-shiryen biyan diyya da sake tsugunar da mutanen da aka tabbatar da sahihancin ikirarin mallakarsu.

 

Kwamishinan kasa da tsara Birane,Abduljabbar Muhammad Umar, ya bayyana hakan lokacin da ya ziyarci garin rimin zakara domin fara aikin tantancewa da sanya alamomin da za su nuna iyakokin filayen jamair bayero wannan matakine da ƙoƙarin gwamnati na kwato tare da kare filayen jami’ar.

 

Kwamishinan ya bayyana cewa bayan kammala aikin tantance iyakokin, za a fara share filayen tare da rushe gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a kan filayen jami’ar, daga bisani kuma gwamnati za ta ɗauki matakin gina katanga da kewaye filayen jami’ar, domin kare su daga sake mamayewa.

 

Kwamishinan yace bayan biyan diyya gwamnatin jahar kano baza ta lamunci dukkanin wata hada-hadar filaye tsakanin Jamiar bayero da garin rimin Zakara ba.

 

Abduljabbar ya kara da cewar matakin gwamnatin na da nufin samar da mafita mai ɗorewa, tare da kare haƙƙin Jamiar bayero da kuma mutanen da suka sayi ko mallaki filaye cikin kyakkyawar niyya.

 

Kwamishinan ya yaba wa mahukuntan Jami’ar Bayero bisa haƙuri, dattako da haɗin kai da suka nuna a lokacin da ake ƙoƙarin warware rikicin. Haka kuma ya gode wa sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma bisa gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da sasanta rikicin.

 

A nasa bangaren, Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero mai kula da harkokin ilimi, Farfesa Ahmad Muhammad Tsauni, ya gode wa gwamnatin Jihar Kano bisa shiga tsakani da kuma jajircewarta wajen kawo ƙarshen rikicin.

 

Farfesa ya bayyana Rimin Zakara a matsayin makwabciyar jami’ar da ke da kusanci, yana mai cewa Jamiar ta dade tana da kyakkyawar alaƙa da al’ummar yankin.

 

Ya kara cewar da dama daga cikin mazauna Rimin Zakara suna aiki a Jamiar, yayin da yaran yankin su ma suke amfana da tallafin karatu da sauran damar samun ilimi da jami’ar ta bayar.

 

Ya bayyana farin cikinsa kan goyon bayan gwamnatin jihar ga aikin sake tantancewa da share filayen jamair, da kuma shirin gina katanga domin kare iyakokin jami’ar daga sake samun kutsen masu mamaye filaye.

 

Ya ce Jamiar Bayero a shirye take ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin Kano da al’ummar Rimin Zakara domin tabbatar da cikakken aiwatar da yarjejeniyar sulhun da aka cimma.

 

Shi ma da yake magana a madadin al’ummar Rimin Zakara, Malam Habu, ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa warware rikicin da ya kwashe kusan shekaru 50 ana fama da shi.

 

Malam Habu ya kara gode wa gwamnan bisa amincewa da biyan diyya ga mutanen da rikicin ya shafa, yana mai cewa adadin kuɗin da aka biya ya fi abin da tun farko aka yi tsammanin za a bai wa masu filayen.

 

Ya ce matakin da gwamnatin ta samar dama ce da Jamiar Bayero da al’ummar Rimin Zakara za su ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya, bayan shafe shekaru masu yawa ana takaddama kan mallakar filayen.

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *