KANO
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Kano ta yi fatali da ƙalubalen da aka gabatar kan huruminta na sauraron ƙarar da wasu ƙungiyoyin Musulunci suka shigar kan Malam Lawan Abubakar Triumph.
Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ne ya jagoranci zaman kotun a ranar Litinin, inda ya saurari hujjojin lauyoyin ɓangarorin biyu kan batun hurumin kotun.
Wasu ƙungiyoyin Musulunci ne suka shigar da ƙarar, inda suka nemi kotun ta umarci Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano da ya gudanar da bincike kan zarge-zargen da suka shafi kalaman da suke cewa sun shafi batanci ga addini.
Lauyan Triumph, Barista Abdurrazak Ahmad, ya ƙalubalanci hurumin kotun na sauraron ƙarar, yana mai cewa akwai batutuwan shari’a da suka shafi ikon masu ƙarar na shigar da ƙarar da kuma kotun da ta dace ta saurari batun.
Ya kuma yi nuni da cewa ƙungiyoyin da suka shigar da ƙarar sun taɓa gabatar da makamanciyar ƙara a wata kotu, tare da kalubalantar sahihancin takardun rajistar ƙungiyoyin da aka gabatar.
Sai dai lauyan masu ƙarar, Barista Aliyu Usman Haji, ya musanta waɗannan hujjoji, yana mai cewa Kotun Shari’a tana da hurumin sauraron ƙarar.
Barista Haji ya kuma gabatar da takardun rajistar ƙungiyoyin ga kotu, yana mai cewa ba a gabatar da su a baya ba ne saboda ba a buƙace su a lokacin.
Bayan sauraron hujjojin ɓangarorin, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya yi fatali da ƙalubalen hurumin kotun, inda ya amince da ci gaba da sauraron ƙarar.
Kotun ta kuma umarci masu ƙarar da su gabatar da kwafen takardun rajistar ƙungiyoyin domin a duba su kafin a sanar da ranar ci gaba da sauraron shari’ar.
A baya, kotun ta ƙi bayar da umarnin rufe masallacin da Malam Lawan Triumph ke jagoranta, tana mai cewa ba ta da hurumin yin hakan.
Ya kamata a lura cewa zarge-zargen da ake yi wa Malam Lawan Triumph ba su zama hukunci ba, kuma har yanzu batun yana gaban kotu domin tantance hujjojin da ɓangarorin za su gabatar
📢 KU BI ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.
📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA
Kira/WhatsApp: +234 803 207 7835
🌐 KAFAFEFENMU
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
