An lalata makarantu fiye da 1000, an kashe malamai 2,295 a Arewa maso Gabashin Nijeriya – In Ji Hukumomi

IMG 115012 03926 1788432624135

Gwamnatin Jihar Borno ta bayyana cewa an lalata makarantu fiye da 1,400 a faɗin yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, yayin da aka kashe malamai 2,295, sannan aka raba mutane 19,000 da gidajensu a tsawon shekarun da aka kwashe ana fama da matsalar ta’addanci da rikici a yankin.

 

Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur ne ya bayyana hakan yayin da yake wakiltar Gwamna Babagana Umara Zulum a wani Taron Tattaunawa na Ƙasa na Kwanaki biyu da aka kan illar Rikici ga Lafiyar Ƙwaƙwalwar Yara a Nijeriya da aka gudanar a Maiduguri.

 

Kadafur ya ce alƙaluman sun nuna mummunan tasirin da rikicin na tsawo lokaci ya yi ga yara, musamman kan lafiyar ƙwaƙwalwarsu da iliminsu da kuma makomarsu a gaba.

 

Ya ce sakamakon tashe-tashen hankulan da aka yi ta fuskanta har bayan samun galaba kan ‘yanta’adda, illar ta kan shafi halayyar yaran da kuma yanayin yarda da amincewarsu da al’ummominsu.

 

“Yanayin damuwa da tsoro ba sa ƙarewa ko bayan an dikile hare-hare. Ya kan shiga ya zauna a cikin ƙwawƙalwarsu da ke bunƙasa. Sai ya sauya yanayin fahimta da ɗabi’u da kuma yardarsu,” in ji shi.

 

Mataimakin gwamnan ya yi gargaɗin cewa raunin da ba a yi masa magani ba zai iya haifar da ɗacin rai da kangarewa da kuma rauni da kan kai ga ɗaukarsu aiki a ƙungiyoyin ‘yanta’adda.

 

Ya ce, ayyuka da shiga tsakani na sojoji kaɗai ba za su iya magance sakamakon tsawon lokacin da aka kwashe na ta’addanci ba, yana mai jaddada buƙatar ƙara shirin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da tallafin zamantakewa a ƙoƙarin samar da yanayin nutsuwa da tsaro.

 

Wakiliyar Mai Ba da Shawara kan Tsaron Ƙasa, Nuhu Ribadu, Daraktan Harkokin Lafiya ta Hukumar Leken Asiri ta Nijeriya, Dr Patience Omokri, ta ce ya kamata a ɗauki mummunan yanayin da yara suka fuskanta a matsayin batun damuwa ga tsaron ƙasa.

 

Ta ce yaran da suka taɓa fuskantar yanayin rashin tsaro da ayyukan ta’addanci, suna fama da ƙuncin rasa iyaye da gidajensu, sannan wasu an yi garkuwa da su, kana wasu sun fuskanci sauran nau’ikan cin zarafi.

 

“Yaron da ya taɓa fuskantar tashe-tashen hankula ba wai kawai wanda aka zalunta ba ne. Idan aka bar shi babu taimako, zai iya zama wani a cikin al’umma da ka iya janyo rashin kwanciyar hankali,” in ji sakon Ribadu.

 

Wakilin UNICEF, Francis Otuochi, ya ce yara 270,864 a Borno da Adamawa da kuma Yobe suna buƙatar kulawar lafiyar ƙwaƙwalwa da ta zamantakewa a ƙarƙashin shirin Majalisar Dinkin Duniya na ɗaukar matakai da buƙatun jin’kai na shekarar 2026.

 

Ya yi kira ga gwamnatoci da su sanya shirin lafiyar ƙwaƙwalwa a cikin tsarin shirye-shiryen kare yara da kiwon lafiya da ilimi da kuma walwalar jama’a.

 

TRT Hausa

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *