Tsaro: Rundunar Yan Sandan Kano Sun Shirya Daruruwan Jami’anta Zuwa Iyakokin Kano 

FB IMG 1788369346712

Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta tura jami’ai 250 da suka kammala horo zuwa kananan hukumomin da ke kan iyakokin jihar, domin karfafa tsaro da inganta daukar matakin gaggawa kan kiran neman dauki.

 

Jami’an sun kammala horon yaki da sarrafa makamai na tsawon wata guda, wanda aka gudanar a sansanonin ’yan sandan Mobile Force na lamba 9 da ke Hotoro da lamba 52 da ke Challawa.

 

Da yake jawabi yayin bikin yaye jami’an, Kwamishinan ’yansandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce tura jami’an na daga cikin dabarun rundunar na karfafa tsaro a kan iyakokin jihar da sauran yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro.

 

Ya umurci jami’an da su kasance masu lura da al’amura, kwarewa da bin doka, tare da amfani da makamai cikin ka’ida da mutunta hakkokin jama’a.

 

Kwamishinan ya bayyana cewa jami’an sun samu horo kan dabarun yaki, sarrafa bindiga, tattara bayanan sirri, gane abubuwan fashewa, amfani da karfi, kare hakkin dan Adam da kuma dabarun aikin ’yansanda tare da al’umma.

 

Ya ce za a ci gaba da gudanar da horaswa na cikin gida domin tabbatar da cewa jami’an rundunar suna da kwarewa da kayan aikin da suka dace wajen gudanar da ayyukansu.

 

Bayan kammala bikin, Bakori ya umarci jami’an 250 da su garzaya wuraren da aka tura su, yana mai cewa matakin zai kara tsaron kan iyakokin Kano, ganin ’yan sanda a wurare daban-daban da kuma inganta martanin rundunar ga barazanar tsaro.

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *