Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamnan Jihar Kano Engr Abba K Yusuf

FB IMG 1738061032326

Daga Abdul Haruna

Mai Girma Gwamna,

KIRA NA GAGGAWA DON DAUKAR MATAKI KAN KARIN WUTAR LANTARKI A JIHAR KANO.

Ina rubuto wannan wasika ne cikin damuwa da kaunar al’ummarmu ta Jihar Kano. Kamar yadda kake sane, zafin rana da ake fama da shi a jihar nan ya kai wani matsayi mai tsanani wanda ke barazana ga lafiyar jama’a, musamman ma ga tsofaffi, kananan yara da masu fama da larurar lafiya musamman masu lalural ciwon laka.

Babbar matsala da ke kara ta’azzara wannan hali ita ce karancin wutar lantarki da jama’a ke fama da ita.Rashin samun wuta yadda ya kamata na hana mutane amfani da na’urorin sanyaya daki,ajiye abinci da

magunguna, da kuma samun ingantaccen yanayi mai sauki a cikin gidajensu. Wannan na iya haddasa cututtukan da suka shafi zafin rana kamar su sankarau, bugun zuciya sakamakon zafi, suma, da kuma karin matsin lamba ga masu ciwon laka, zuciya da hawan jini.

Mai Girma Gwamna, lokaci ya yi da za a dauki mataki na gaggawa. Kamar yadda ake fadi, “rigakafi ya fi magani araha.” Muna rokonka da ka yi duk mai yiwuwa ta hanyar tattaunawa da gwamnatin tarayya,KEDCO don inganta cibiyoyin rarraba wuta domin kara yawan wutar lantarki da ake samu a Jihar Kano.

Mutanen Kano masu juriya ne, amma ba za a bar su su sha wahala ba yayin da ake da damar hana hakan.Ina da kwarin gwiwa cewa Mai Girma Gwamna za ka ci gaba da nuna jagoranci da kishin al’umma, kamar yadda aka san ka da shi tun farko.

Ina rokon Allah Ya sa wannan takardar ta isa ga Mai Girma Gwamna don taukar mataki cikin gaggawa.

Da girmamawa,

Engr Abdul Haruna,

Mai Kishin Kano.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *