Da Dumi Duminsa: Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta bukaci hukumomi a Najeriya su kama Sheikh Jingir 

IMG 164813 11826 1786463302168

Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Ƙasa (NHRC) ta nemi hukumomin tsaro da su kama tare da gurfanar da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir, kan kalaman da ya yi game da tikitin Musulm-Musulmi na jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

 

Alfijir labarai ta rawaito, Sakataren zartarwa na ƙungiyar, Tony Ojukwu, SAN, ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya buƙaci Babban Sufeton ’Yan Sanda, da Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS), da sauran hukumomin da abin ya shafa su ɗauki mataki kan malamin.

Wani Labarin: Yunwa Da Rashin Tsaro: Ya Kamata Gwamnati Ta Yi Abin Da Ya Dace —In Ji Sheikh Jingir

Ƙungiyar ta bayyana cewa kalaman Sheikh Jingir na iya ƙara rura rikicin addini da raba kan al’umma, musamman a lokacin da Najeriya ke shirin shiga zaɓen 2027.

 

Ƙungiyar ta ce ɗaukar mataki zai zama darasi ga waɗanda ke son amfani da addini wajen cimma muradun siyasa.

 

Sheikh Jingir ya bayyana matsayinsa na goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi a 2027 ne yayin wani taron bikin aure na gama-gari da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya, inda ya kuma yi kira ga Musulmi su shirya domin zaɓen.

Wani Labarin: Innalillahi wa Inna Ilaihirraji’un! Allah ya yiwa Sheikh Jingir Rasuwa

Kalaman sun jawo martani daga wasu ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki, yayin da ake ci gaba da muhawara kan tasirin addini a siyasar Najeriya.

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *