Daga Ranar Da Aka Zaɓe Ni Zan Soke Dokar Fanshon Gwamnoni A Kano — In Ji Ibrahim Little

IMG 183336 09826 1786296852724

Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Alhaji Ibrahim Ali Amin Little, ya bayyana cewa zai soke dokar da ta bawa tsofaffin gwamnoni damar karɓar fansho da wasu alawus-alawus, idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar a 2027.

Little ya bayyana hakan ne a yau Lahadi a Kano, yayin wani taron manema labarai, inda ya kuma sanar da zaɓen Abdulkadir Shehu Bari daga Ƙaramar Hukumar Rogo a matsayin abokin takararsa na mataimakin gwamna.

Ya kara da cewar daga ranar da aka zaɓe shi ya hau kujerar gwamna, zai ɗauki matakin sake duba dokokin da suka shafi biyan tsofaffin gwamnoni fansho, yana mai cewa ana amfani da tsarin wajen karkatar da dukiyar jama’a.

Ɗan takarar ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen tabbatar da cewa kuɗaɗen jihar sun fi karkata ne zuwa ayyukan da za su inganta rayuwar al’umma, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi da ƙarfafa matasa da mata.

Ya kuma yi alkawarin magance matsalolin da suka addabi fannin ilimi da lafiya, tare da samar da shirye-shiryen tallafa wa marasa galihu, musamman zawarawa, marayu da yaran da ba sa zuwa makaranta.

Little ya ce gwamnatinsa za ta ƙarfafa harkokin kasuwanci da ƙirƙire-ƙirƙire ta hanyar samar da cibiyoyin sana’o’i da kasuwanci a sassa daban-daban na jihar.

A cewarsa, shirin zai taimaka wajen sauya Kano daga al’umma mai yawan dogaro da shigo da kayayyaki zuwa jihar da ke samarwa, samar da ayyukan yi da kuma ƙirƙirar arziki.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta yi aiki da tsarin mulkin kowa da kowa, tare da bai wa ‘yan ƙasa damar shiga cikin harkokin ci gaban jihar ba tare da la’akari da matsayinsu ko asalinsu ba.

Al-Amin ya yi kira ga al’ummar Kano da su bai wa jam’iyyar ADC goyon baya a zaɓen 2027, yana mai cewa manufofinsa sun mayar da hankali ne kan inganta rayuwar jama’a da kuma tabbatar da amfani da dukiyar jihar wajen amfanin al’umma.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *