A safiyar asabar ne gwamnan Jahar Kano, Alh. Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci taron Saukar Al’ qur’ani mai Girma da kuma addu’o i na musamman tare da mahaddata alƙur’ani sama da Dubu Hudu da Dari Hudu da Arba’in da Hudu 4,444, domin ƙara tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Kano da Najeriya baki daya
Wannan babban taro ya kasance abin taɓa zuciya, ganin irin ɗumbin jama’a da suka taru da niyyar neman taimakon Allah, kuma hakan ya nuna muhimmancin addu’a musamman a wannan lokutan da muke fuskantar ƙalubale iri iri
Babban Director General na hukumar Shari’ah ta jihar Kano, kuma mamba a hukumar Alhazzai, babban limamin masallacin juma’a na kofar Nassarawa Dr sani Ashir ne ya jagoranci sallar la’asar tare da gabatar da alkunuti bayan kammala saukar.
Wannan taron addu’ar, ya zo ne akan ƙarin jajircewar da Gwamna Abba Kabir Yusuf yake yi wajen tallafawa hukumomin tsaro da kayan aiki, da kuma sauran tallafi domin cigaba da ƙarfafar jami’an tsaro akan yaki da rashin tsaro. Kuma wannan wata yar manu niya ce wajen tabbatar da kishin da Gwamna Ya ke da shi wajen cigaban Jihar Kano da kuma al’ ummar ta
Jama’a daga kowane sassa na jihar Kano sun halarta, sun kuma shafe tsawan wuni guda, a na Karatu, da kuma addu’oi don neman Allah Ya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da barazar zaman lafiya
Muna rokon Allah Ya karba ma na wannan addu’oi, da kuma Allah Ya yi mana gammakatar Ya kuma karbi wannan ibada da mu kai
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835











https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
