Gwamnatin Najeriya ta amince da kashe Biliyan 46 domin gyaran titin jirgin sama na Malam Aminu Kano

FB IMG 1785327306038

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da ware Naira biliyan 46 domin gyara manyan hanyoyin sauka da tashin jiragen sama (runways) na Mallam Aminu Kano International Airport tare da inganta tashar jiragen cikin gida ta filin jirgin.

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya sanar da hakan yayin ƙaddamar da sabuwar tashar cikin gida ta Dankabo da aka inganta a filin jirgin na Kano.

A cewarsa, aikin zai ƙara inganta tsaro, sauƙaƙa zirga-zirgar jiragen sama, da kyautata jin daɗin fasinjoji, tare da ƙarfafa matsayin Kano a matsayin babbar cibiyar sufurin jiragen sama a Arewacin Najeriya.

Gwamnatin ta ce wannan na daga cikin shirinta  inganci, tsaro da kuma ayyukan sufurin jiragen sama.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *