Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Jihar Kano kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Safarar Haramtattun Ƙwayoyi, Muhuyi Magaji Rimin-Gado, ya yi kira ga ’yan siyasa da su daina tsoma baki wajen neman a saki mutanen da aka kama da zargin ayyukan daba ko laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi.
Rimin-Gado ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin taron manema labarai da ya gudanar a Kano, inda ya ce kwamitin ba zai bari wani matsin lamba daga masu ruwa da tsaki ya hana shi aiwatar da aikinsa yadda doka ta tanadar masa ba.
Ya ce manufar kwamitin ita ce yaƙi da shan da safarar miyagun ƙwayoyi da kuma daƙile ayyukan ’yan daba domin tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.
“Ina gargaɗin duk wani ɗan siyasa da kada ya zo wajena yana neman a saki wani ɗan daba idan muka kama shi. Wannan Kano tamu ce, kuma dole ne mu haɗa kai wajen kare ta. Ba za mu bari wasu tsirarun mutane su ci gaba da lalata rayuwar matasanmu da zaman lafiyar al’umma ba,” in ji Rimin-Gado.
Ya ƙara da cewa mutum ɗaya tilo da zai iya ba shi umarnin sakin wanda aka kama shi ne Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
“A ranar da gwamna ya ce in saki wani da aka kama, hakan zai zama alamar cewa lokaci ya yi da zan ajiye wannan muƙami,” in ji shi.
Kwamitin haɗin gwiwar, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar, ya haɗa wakilan hukumomin tsaro daban-daban, kuma an kafa shi ne domin ƙarfafa yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ayyukan ’yan daba a jihar.
Rimin-Gado ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro da kwamitin haɗin kai ta hanyar kai rahoton duk wani da ake zargi da aikata laifuka, yana mai cewa haɗin kan jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
