Gwamnatin Najeriya ta fara rabon tallafin biliyan 75, bashi ga ƙananan ƴan kasuwa

best seller i

Temitola Adekunle-Johnson, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan samar da ayyukan yi da kanana da matsakaitan masana’antu (MSMEs), ya ce gwamnatin tarayya ta fara raba tallafin bashin naira biliyan 75 mai kashi daya cikin dari ga kanana da matsakaitan masana’antu ta  hanyar Bankin Masana’antu (BOI).

Alfijir labarai ta rawaito cewa Adekunle-Johnson ya yi bayanin hakan a ranar Laraba yayin wani taron kewayen kasa don wayar da kan kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa kan shirin bayar da tallafin shugaban kasa da bashin a Abuja.

A ranar 29 ga Oktoba, Olusegun Dada, mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafofin sada zumunta, ya sanar da hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da BOI don tallafa wa kananan ‘yan kasuwa 75,000 da bashin naira miliyan daya kowanne.

Dada ya ce bashin yana dauke da ragin kashi daya cikin dari. A cewar Adekunle-Johnson, ‘yan kasuwar za su iya ziyartar kowanne reshen BOI domin neman bashin.

“A yanzu haka muna da taron a jihohin Ogun, Bauchi, Enugu, da Kaduna a lokaci daya. A cikin shekarar 2023, Shugaba Bola Tinubu ya amince da wasu kudade a matsayin tallafin rage radadin cire tallafin mai,” in ji mai taimaka wa shugaban ƙasa.

The Cable

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

One Reply to “Gwamnatin Najeriya ta fara rabon tallafin biliyan 75, bashi ga ƙananan ƴan kasuwa”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *