A cikin ƙoƙarinsa na rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da ƙananan yara, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake ƙaddamar da Asibitin Nuhu Bamalli bayan gyare-gyare masu yawa da gwamnatinsa ta gudanar.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.
Da yake jawabi ga ma halarta bikin ƙaddamar da asibitin a ranar Alhamis, Gwamnan ya bayyana gamsuwarsa da cigaban da aka samu a cikin asibitin.
Ya bayyana cewa bayan karɓar mulki, asibitin yana cikin halin lalacewa, kuma yana cikin wuraren da ya bai wa muhimmanci na farko wajen ingantawa.
“A yau, sakamakon wannan jajircewar ya zama gaskiya.”
Gwamna Yusuf ya ja hankalin masu ruwa da tsaki a asibitin su kula da kayan aikin da aka saka tare da kiyaye tsabtar asibitin, inda ya yi nuni da muhimmancin samar da ingantaccen kula na lafiya ga al’ummar Kano.
Ya sake tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa na da himma wajen samar da kyakkyawan yanayi na kula da lafiya.
Dangane da wannan hangen nesa, ya bayyana cewa an riga an bayar da kwangilar gyaran dukkan manyan Asibitoci a jihar domin amfanin al’umma gaba ɗaya.
A lokacin taron, Gwamnan ya raba kayan kula na lafiya masu muhimmanci ga asibitoci a fadin jihar Kano.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
