Shugaba Donald Trump ya ce ya kamata ya kasance yana cikin waɗanda za su zaɓi sabon shugaban jagoran addinin Iran.
Trump ya bayyana haka ne a zantawarsa da kafar yada labarai ta Axios, inda ya ce yana kyautata zaton jamhuriyar Musuluncin ta Iran za ta zaɓi ɗan marigayi Ayataullah Khamna’i, wato Mojtaba Ali Khamna’i a matsayin sabon jagora, amma Trump ya ce lamari ne da ba zai taɓa amincewa da shi ba.
Har yanzu cibiyar ƙwararru, wadda ita ce ke da alhakin naɗa sabon jagoran, ba ta sanar da wanda zai gaji Ayatollah Ali Khamna’i ba, wanda harin Amurka da Isra’ila ya kashe a ranar Asabar a birnin Tehran.
Kawo yanzu ba a sanar da ranar da za a yi jana’izar marigayin ba, bayan ɗagewar da hukumomi suka yi a farkon makon nan saboda fargabar turmutsutsu a sanadiyar tururuwa ake tunanin mutane za su yi a wajen binne marigayin.
BBC
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
