Majalisar Tuntuba ta Masu Ruwa da Tsaki ta Karamar Hukumar Garko ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da su fifita cancanta, mutunci, da kuma tarihin da aka tabbatar wajen zaÉ“ar ‘yan takara don tsayar da su mukaman zaÉ“e na jiha da tarayya, a matsayin wani É“angare na Æ™oÆ™arin tabbatar da wakilci mai inganci ga al’ummar Æ™aramar hukumar Garko.
An yi wannan kiran ne a lokacin wani zaman tattaunawa na masu ruwa da tsaki na manyan jami’ai da aka gudanar a Kano, inda Shugaban Æ™ungiyar, Hamisu Sule Garko, ya jaddada cewa zamanin tsayar da shalelen wasu mutane shugabanci ya zo Æ™arshe.
Ya ce kungiyar wacce ta Æ™unshi masu fasaha, masu riÆ™e da mukamai na gwamnati da shugabannin kasuwanci, da ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, ya himmatu wajen haÉ“aka sabon tsarin shiga siyasa don cigaban al’umma.
“Kungiyar mu ta tuntuba ta Dattawan karamar hukumar Garko ta jaddada cewa dole a samu sauyi a yanayin da ake fitar da ‘yan takara. Muna rokon dukkan ‘jam’iyun siyasa da su tsayar da mutanen da suka cancanta don wakiltar yankinmu,” inji Hamisu Sule.
A cewarsa, kungiyar tuntuba ta al’ummar yankin, ayyukan ya ta’allaka ne akan imanin cewa ci gaba mai dorewa yana da alaÆ™a kai tsaye da ingancin shugabanci, yana mai Æ™ara da cewa Garko tana da tarin mutane masu Æ™warewa waÉ—anda za su iya wakiltar yankin yadda ya kamata a matakin jiha da Æ™asa.
Ƙungiyar ta Æ™ara jaddada Æ™udurinta na gano da tallafawa mutane masu halaye na gari, tana mai lura da cewa jagoranci mai inganci yana da matuÆ™ar muhimmanci don jawo ci gaba mai ma’ana ga yankin.
> “Manufarmu ita ce mu yi tunani da kuma gano mutanen da suka tabbatar da gaskiya. Mun yi imanin cewa shugabanci mai Æ™warewa ne kawai a kowane mataki zai iya jawo ci gaban da ake buÆ™ata ga al’ummarmu. A nan gaba, GSCC za ta yi aiki a fannoni daban-daban na jam’iyya don tabbatar da cewa Garko ba ta sake zama a baya ba, amma tana wakiltar shugabanni waÉ—anda suka fahimci radadi da burin mutanenta,” in ji shugaban.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa taron ya sake jaddada alƙawarinta na bayar da shawarwari wanda ke haɓaka shugabanci mai kyau da ci gaban tattalin arziki, ba kawai a cikin Ƙaramar Hukumar Garko ba, har ma a faɗin Jihar Kano gaba ɗaya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
