Majalisar dokokin Amurka ta gargadi  shugaban Amurka kan ya daina yaƙi a Iran

IMG 135757 04626 1780577898518

Majalisar wakilai ta Amurka ta kaɗa ƙuri’a inda ta umarci Shugaba Donald Trump ya janye sojojin Amurka daga yakin Iran, ko kuma ya nemi amincewar majalisun dokokin ƙasar kan ci gaba da yaƙin.

Ƴan majalisar daga jam’iyyar Republican huɗu sun goyi bayan ƴan Democrats wajen amincewa da wannan mataki wanda yanzu zai wuce zuwa majalisar dattawan ƙasar.

Matakin da aka ɗauka dai ya kasance na je-ka na yi-ka ne a yayin da shugaban ƙasa ke da ikon hawa kujerar na-ƙi a kan duk wani hukunci ko matakin da ya ga zai ka wo masa matsala a shugabancinsa.

Wannan shi ne matakin na baya-bayan nan na kara nuna adawa da matakin Trump din a kan Iran, daga cikin jam’iyyarsa ta Republican.

BBC

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *