Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 24, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Mahmud, ta ba da umarnin kamo Hon. Aliyu Ibrahim Haidar duk inda yake domin gurfanar da shi a gaban kotu.
Tun da farko, Gwamnatin Jihar Kano ce ta shigar da ƙara a kansa bisa zargin damfara, cuta da kuma sayar da kadarorin bogi da suka haɗa da filaye, kangaye da gidaje da darajarsu ta kai kimanin naira miliyan 134 ga wani mutum mai suna Alhaji Sani Abdullahi a unguwannin Dan Bare, Kuyan Ta Inna da kuma yankin Kantitin zuwa Sani Abacha Youth Centre.
Sai dai a zaman kotun na yau Litinin, wanda ake ƙarar bai halarci kotun ba duk da cewa an sanar da shi ranar shari’ar.
Lauyan Gwamnatin Jihar Kano, Barista Zahraddeen Hamisu Kofar Mata, ya roƙi kotun da ta bayar da umarnin kama Aliyu Ibrahim Haidar, yana mai cewa ya yi watsi da umarnin kotu duk da kasancewarsa cikin masaniyar ranar shari’ar, kuma jami’in kotu ya isar masa da takardar gayyata.
Bayan sauraron ƙorafin, kotun ta amince da buƙatar tare da bayar da umarnin kamo wanda ake ƙarar, sannan ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Yuli, 2026.
freedom Radio
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t