Tsohon gwamnan jihar Kano, Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa ba zai daina siyasa ba muddin yana da karfi da lafiya. Ya yi wannan bayani ne a yayin taron manema labarai da ya gudana a ranar Laraba 05 ga Nuwamba, a fadarsa ta Mundubawa a Kano, inda ya ce shi ya dauki siyasa ne a matsayin hanyar hidimtawa al’umma, ba wai neman matsayi ba.
Shekarau ya jaddada cewa duk ayyukan sa na siyasa suna bisa ginshikin halin kirki, jajircewa, mutuntawa, hakuri da dogaro ga Allah, wadanda ya bayyana a matsayin muhimman ka’idojin da suka jagorance shi wajen samun nasara a rayuwa.
A cikin jawabinsa, Shekarau ya nemi jama’a su yi masa afuwa idan akwai wanda ya taba batawa, tare da bayyana cewa shi ma ya yafe wa duk wanda ya taba yi masa laifi. Ya yi kira da a kara karfafa zumunci, yafiya da hadin kai, yana mai cewa zaman lafiya ba zai tabbata ba idan jama’a suka kasa rungumar juna.
Tsohon gwamnan ya kuma bukaci shugabanni su mai da hankali kan farfado da rayuwar talakawa, yana mai cewa zaman lafiya da ci gaba ba sa tabbata idan yunwa ta yi kamari a cikin al’umma. Ya ce duk shekarar da Allah ya kara masa a bayan 70, yana kallonta a matsayin wata ni’ima ce daga Allah, wanda zai yi amfani da shi wajen ci gaba da hidimta wa al’umma.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t