Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar sanya tsattsauran takunkumin tattalin arziki kan duk wata ƙasa da ta yi hulɗar cinikayya da Iran.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Laraba, Trump ya ce, Iran za ta ɗanɗana kuɗarta domin kuwa zai ƙakaba mata “matakan matsin tattalin arziki mafiya muni” tun da ta ƙi amincewa da buƙatunsa na miƙa wuya.
“Duk ƙasar da ta bari cibiyoyin kuɗinta da harkokin kasuwancinta da filayen jiragen samanta ko hukumomin gwamnati suka sauƙaƙa wa Iran, za ta fuskanci mummunan sakamako a fannin tattalin arziki,” in ji shi.
Ba wannan ne karon farko da Trump yake yi wa Iran barazana ba, sai dai Iran ta sha cewa ba za ta daina yaƙi da Amurka ba sai an cika sharuɗɗan da ta gindaya.
TRT Hausa
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
