Jam’iyyar adawa ta APC reshen jihar Zamfara ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta baci a jihar domin bada damar samun nasarar yaki da ayyukan ‘yan fashin daji.
Alfijr Labarai ta rawaito cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Yusuf Idris ya fitar, APC ta yi zargin cewa Gwamna Dauda na yin zagon kasa a kokarin gwamnatin tarayya na yaki da ‘yan fashin daji a jihar saboda “baya son tsohon Gwamna Bello Matawalle ya yi nasara”.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa, Gwamna Lawal na son yakin da ake da ƴan fashin daji, wanda ya fara haifar da sakamako mai kyau, kar ya yi nasara saboda dalilai na siyasa.
Sanarwar ta ce: “Yakin da ake yi da ‘yan fashin daji a jihar Zamfara wanda sojoji ke yi a yankin Arewa maso yamma karkashin jagoranci da sanya idon karamin ministan tsaro, Bello Matawalle bisa umarnin shugaban kasa Tinubu yana haifar da sakamako mai kyau da ba a saba ganin sa ba.”
“Kokarin gwamnatin tarayya na yaki da ‘yan fashin daji abin a yaba ne kuma akwai bukatar a ci gaba da shi a kowanne yanayi domin yankin ya kubuta daga bata gar1”.
APC ta kuma soki Gwamna Dauda kan gazawa a fannin tsaro a shugabancin jihar.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
