Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta samu nasara wajen yaki da laifuka, bayan kama mutane biyar da ake zargi da fashi da makami tare da kwato bindigar Tokarev guda daya da harsasai 48 masu rai kirar 7.62mm. An kwato makaman ne bayan jami’an Dorayi Babba sun samu bayanan sirri daga wani dan kasa. Africans & Diaspora
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewar sanarwar a wani samame a Karamar Hukumar Rogo, jami’an ’yan sanda sun kama mutane biyar da ake zargi da hannu a wasu hare-haren fashi da makami a kauyen Jajaye da kewayenta. Rundunar ta ce wadanda ake zargin sun amsa hannu a satar babura kusan biyar da wasu kayayyaki masu daraja.
Haka kuma, jami’an ’Yan Sandan Gaya sun kwato wata saniya da rago da aka ruwaito cewa an sace, tare da kama wasu mutane da ake zargi da safarar dabbobin. Bincike ya kuma kai ga cafke wasu mutane biyu da ake zargi mambobin kungiyar masu satar dabbobi ne.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike kan wadanda aka kama domin gano sauran mutanen da ake zargi suna da hannu a laifukan, yayin da wasu daga cikin wadanda ake zargin aka gurfanar da su a gaban kotu. Za a gurfanar da sauran wadanda ake zargin bayan kammala bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa jami’an rundunar da kuma al’ummar jihar bisa hadin gwiwa da samar da bayanan sirri.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
