Daga Aminu Bala Madobi
Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaben fidda gwani na Jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar 16 ga watan Mayu domin neman ɗan takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Balanga/Billiri.
Kotun ta yanke hukuncin cewa zaben bai bi wasu tanade-tanaden da Dokar Zabe ta ƙasa ta shimfiɗa ba. Haka kuma, ta umurci APC da ta sake gudanar da sabon zaben fidda gwani.
Mai shari’a Vera Ibrahim ta kuma hana Ali J.C., wanda ya yi nasara a zaben da aka soke, shiga sabon zaben fidda gwani.
Kotun ta bayyana cewa sunan Ali bai kasance cikin kundin rajistar ’yan jam’iyyar APC da aka miƙa wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) cikin wa’adin da doka ta tanada ba.
Rahotanni sun ce Ali ya koma APC ne kwanaki 16 kacal kafin gudanar da zaben fidda gwani.
Alkaliyar kotun ta dogara da sashe na 77 na Dokar Zabe, wanda ya tanadi cewa dole ne jam’iyyun siyasa su miƙa wa INEC kundin sunayen ’yan jam’iyyarsu aƙalla kwanaki 21 kafin gudanar da zaben fidda gwani.
Justice Ibrahim ta ce batun da ke gaban kotun ba wai kawai ko Ali ɗan APC ne ko ba ɗan APC ba ne, illa tambayar ko jam’iyyar ta bi ƙa’idar doka wajen miƙa kundin sunayen ’yan jam’iyyarta ga INEC a lokacin da doka ta tanada.
A hukuncin nata, kotun ta ce APC da INEC ba su gabatar da isassun hujjoji da za su tabbatar da cewa sunan Ali yana cikin kundin rajistar da aka miƙa wa INEC cikin wa’adin da doka ta tanada ba.
Daga nan ne kotun ta soke zaben fidda gwani na ranar 16 ga Mayu, tare da umurci APC da ta sake gudanar da sabon zaben fidda gwani bisa tanade-tanaden Dokar Zabe. Hukuncin ya sake jefa wakilcin APC na mazabar Balanga/Billiri cikin rashin tabbas yayin da ake tunkarar babban zaben 2027.
Bayan yanke hukuncin, lauyan mai ƙara, Ibrahim Aliyu, ya bayyana cewa hukuncin ya sake tabbatar da muhimmancin bin tanade-tanaden Dokar Zabe wajen gudanar da zabukan cikin gida na jam’iyyun siyasa.
📢 KU CI GABA DA BIN ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sabbin labarai, rahotanni, bincike, shirye-shirye da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
📞 TUNTUBE MU
Domin samun ƙarin bayani, turo mana da labari, haɗin gwiwa, tallace-tallace, ɗaukar nauyin shirye-shirye ko wasu buƙatu:
📱 +234 803 207 7835
📰 Kuna da labari ko wani muhimmin bayani?
Ku turo mana da labaran gaggawa, sanarwar hukumomi, jawabi, sanarwar taro da abubuwan da suka shafi al’umma domin tantancewa da yaɗawa.
🤝 KU YI HAƊIN GWIWA DA MU
Muna maraba da mutane, ƙungiyoyi, hukumomi da ‘yan kasuwa masu sha’awar:
• Haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai
• Tallace-tallace
• Daukar nauyin shirye-shirye
• Haɗin gwiwar kamfanoni da hukumomi
• Rahotanni na musamman da bincike
• Tallata taruka da shirye-shirye
📞 Domin tattaunawa:
+234 803 207 7835
🌐 KU BI MU A KAFAFEN SADA ZUMUNTA
🐦 X (Twitter):
“Ku bi mu a X” https://twitter.com/Musabestseller?s=09
📘 Facebook:
“Ku bi mu a Facebook” https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
🧵 Threads:
“Ku bi mu a Threads” https://www.threads.net/@alfijirlabarai
▶️ YouTube:
“Ku yi Subscibe a YouTube https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
📸 Instagram:
“Ku bi mu a Instagram” https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 SHIGA GROUP WHATSAPP
Ku kasance cikin masu samun sabbin labarai, shirye-shirye, rahotanni da muhimman sanarwa kai tsaye ta WhatsApp.
👇👇
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f?s=cl&p=a&mlu=4&ilr=4
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
📰 Labarai • Rahotanni • Bincike • Shirye-shirye • Wayar da Kai
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
