Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar gaggawa ta hana daba da shaye-shaye a jihar

FB IMG 1778588658214

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da kwamitin haɗin gwiwa na hukumomi da dama domin yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi tare da sanya hannu kan wata dokar gaggawa da ke da nufin dakile ayyukan daba da sauran laifukan da ke da alaƙa da su a faɗin jihar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa shan miyagun ƙwayoyi na ɗaya daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar matasan Kano, yana mai cewa matsalar na haddasa aikata laifukan tashin hankali, rusa iyalai, raunana tattalin arziki da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma.

Ya ce sabon kwamitin zai jagoranci ƙoƙarin gwamnati wajen yaƙi da matsalar ta hanyar tattara bayanan sirri, aiwatar da doka, wayar da kan jama’a, kula da masu shaye-shaye da haɗa kai da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta samar wa kwamitin isassun kuɗaɗe, motocin aiki, ofisoshi, kayan aiki da kariyar tsaro, tare da ba shi cikakken ‘yancin gudanar da aikinsa ba tare da katsalandan ba.

Hakazalika, ya ce gwamnati za ta ci gaba da faɗaɗa cibiyoyin gyaran hali ga masu fama da shan miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa an riga an kafa cibiyoyi daban-daban na maza da mata domin taimaka musu su warke tare da komawa cikin al’umma.

Gwamnan ya ce dokar gaggawa ta hana daba za ta ƙarfafa tsarin doka wajen tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifi, rage rikice-rikicen siyasa da kuma tallafa wa hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Da yake karɓar wannan nauyi, shugaban kwamitin, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado, ya gode wa gwamnan bisa amincewar da ya nuna masa da sauran mambobin kwamitin.

Ya yi alƙawarin gudanar da aikin cikin gaskiya, ƙwarewa da adalci, tare da haɗa kai da hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ƙungiyoyin fararen hula, cibiyoyin ilimi da shugabannin al’umma domin yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da inganta zaman lafiya a Kano.

A ƙarshe, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci al’ummar jihar su ba kwamitin haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da kuma haɗa kai da jami’an tsaro, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa haɗa Dokar Zartarwar da ayyukan kwamitin zai taimaka matuƙa wajen rage laifukan da ke da alaƙa da miyagun ƙwayoyi da kuma samar da Kano mai zaman lafiya da ci gaba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *