…Wajibi a cusawa yan Najeriya son kasarsu domin da yawa basu san alherinta da amfanita ba…
Malam Ibrahim Khalil ya bayyana haka yayin wata karramawa da ƙungiyar Wazobia Conflict Resolution And Peace Advocacy Initiative Wacorpal ta yi masa a Kano.
Ƙungiyar ta karrama Malam Ibrahim Khalil ne da lambobin yabo na Conflict Management Campion da kuma Global Peace Ambassador Award
Malam Khalil ya bayyana cewar babu abinda muke bukata a Najeriya kamar haɗin kai
Idan ka kalla asalin Najeriya a baya akwai haɗin kai da alaƙa mai ƙarfi wanda yanzu wasu suke ta kokarin sai sun kawo sabani a tsakanin ƴan ƙasa.
Don haka ya zama wajibi a cusawa yan Najeriya son Najeriya! Domin da yawa basu san alherin ta ba da darajar ta tare da amfanita ba. Idan ka kalli ƙasar Ruwanda bata sami zaman lafiya ba, sai da ƴan sandan Najeriya suka je suka samar da zaman lafiya, wannan shine ya kawo zaman lafiya a kasar, kun ga kuwa dole muma muyi kokarin samar da zaman lafiya a cikin ƙasarmu, duba da cewa tsatso daya muka fito wato Annabi Adam da Hauwau, kun ga kuwa yan uwan juna ne mu, ko da kuwa da bambancin addini ko bangaranci.
Idan takamarka addini takamarka ka tafi Makka ko Batikan ko Jelle salam ba musulmi ne yake kera jirgin ba, yawan cinsu ma basu da addini, don haka kowa yana buƙatar kowa, mu kalli jin kai da girmama juna shine zaman lafiyar mu.
Kuma Allah ya ce na halicciku ne daban-daban domin mu fahimci juna, mu kyautatawa juna. Don haka muna fata a yi kokarin saka yan Najeriya a kyakkyawan hanya domin son juna.
Akarshe Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana kungiyar Wazobia Conflict Resolution And Peace Advocacy Initiative Wacorpal a matsayin ƙungiyar da ta dace da cigaba da hada kan ƴan Najeriya da samar da sulhu da zaman lafiya tsakani.
A nasa bangaren shugaban kungiyar ta Wazobia Conflict Resolution And Peace Advocacy Initiative Wacorpal Amb. Dr Garba Sulaiman ya bayyana cewar sun zaɓi baiwa Malam Ibrahim Khalil wannan kyaututtukan ne domin ganin irin yadda yake fatawa ta wayewa da kokarin hada kan musulmi da kiristoci da kuma al’ummar Najeriya da ta Duniya baki daya.
Don haka suka ga aikin ƙungiyar su yayi kamanceceniya da ayyukan Malam, wannan takara musu kwarin gwuiwar yi masa wannan ƙarancin.









Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
