Gadar dai ta shafe fiye da shekaru hamsin al’ummar yankin da makiyaya na amfanar ta, yayin tsallaka babban titin domin kauce wa faruwar hatsari.
Daukar matakin dakatarwar ya zo ne sakamakon koke-koken da al’ummar da ke zaune a yankin suka shigar ma’aikatar kasa da tsara birane kan yadda wasu ke kokarin rusa gadar ba tare da yarjewar gwamnati ba.
Kwamishinan ma’aikatar kasa da tsara birane na jihar, Abduljabbar Muhammad Umar Garko ne, ya jagoranci aikin dakatar da rushe gadar tare da kama wadanda ake zargi da hannu a lamarin.
Yayin da yake jawabi a wurin, kwamishinan ma’aioatar kasar ya bukaci al’umma su cigaba da sanar da su, duk wani aiki da ya saba da doka ga hukumomin da suka dace, tare da gargadin cewa wasu mutanen na yaudarar jama’a kan cewa suna da izinin gwamnati, alhali ba Su da wani izini daga bangaren gwamnatin.
Kwamishinan, ya jaddada cewa gwamnatin jihar Kano ba za ta amince da duk wani yunkuri na lalata kadarorin al’umma ko na gwamnati ba, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu a irin wannan badakala zai fuskanci fishin hukuma
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
