Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wata matashiya mai shekaru 25 da ake zargi da yanke mazakutar saurayinta a wani otal da ke unguwar Badawa a Kano.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Litinin, bayan da suka samu rahoton abin da ya faru.
Ya ƙara da cewa bayan faruwar lamarin, matar ta yi ƙoƙarin kai saurayin zuwa banɗaki domin tsaftace jinin da ya zuba kafin mutanen da ke kusa suka gano abin da ya faru tare da sanar da jami’an tsaro.
Dangane da jita-jitar cewa an yi amfani da wani sinadari ko kayan maye kafin aukuwar lamarin, kakakin rundunar ya ce har yanzu babu wata hujja da ke tabbatar da hakan.
Ya ce jami’an ’yan sanda sun samu kwalbar abin sha da ruwa a cikin ɗakin otal ɗin, kuma ana ci gaba da bincike domin gano ko suna da alaƙa da abin da ya faru.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa saurayin yana raye kuma yana samun kulawar likitoci a wani asibiti.
A halin yanzu, wadda ake zargin tana tsare a hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da ita a gaban kotu.
ANZO WAJEN
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
