Gwamnatin jihar Kano ta karkashin ma’aikatar lafiya, ta umarci hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu PHIMA, da ta kulle dukkan wani asibitin kudi da ke yin aiki ba tare da ya yi Rijista ba.
Kwamishinan lafıya Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bada wannan umarni yayin da ya ke bude taron bita da bada horo ga shugabanni da mamallaka asibitoci masu zaman kansu da ke nan Kano wanda hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu PHIMA ta shirya, ake gudanar da shi yanzu haka a yau Alhamis.
Ya ce, daukar wannan mataki ya zama dole sakamakon yadda ake samun matsaloli wajen yadda asibitocin ba sa gabatar wa gwamnatin bayanan ayyukansu kama daga alkaluma da bayanan mutanen da suka duba da sauransu.
Kwamishinan, ya kara da cewa, “A yanzu haka mutane da dama sun zabi rika tafiya asibitoci masu zaman kansu maimakon na gwamnati domin neman lafiya, sai dai da da dama daga cikin irin wadannan asibitoci ba su da Rijista.
Don haka daga yanzunan, ina mai sanar da bayar da umarnin kulle duk wani asibiti da ke gudanar da aiki ba tare da cikakkiyar rijistar gwamnati ba.”
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
