Iran ta kashe sojojin Amurka biyu, yayin da Trump ya ba da umarnin kai mata hare-hare

IMG 135757 04626 1780577898518

Hare-haren makamai masu linzami da jirage mara matuƙa na Iran sun kashe akalla sojojin Amurka biyu tare da ɓatar da wani sojin Amurkan a ƙasar Jordan.

A saƙon da ta wallafa a shafinta na X, hedikwatar tsaron Amurka (CENTCOM) ta tabbatar da cewa wannan lamarin ya auku ne ranar 17 ga watan Yuli yayin da dakarun Amurka da na Jordan ke famar daƙile hare-haren Iran.

Kazalika saƙon ya ƙara da cewa an garzaya da sojojin Amurka huɗu asibitocin ƙasar Jordan, tana mai ƙarawa da cewa tuni aka sallami sojojin daga asibitocin.

Saƙon kuma ya ce waɗanda aka tatbbatar cewa ba su ji rauni da yawa ba sun koma bakin aiki.

“Saboda girmamawa ga iyalan [waɗanda lamarin ya shafa], CENTCOM za ta riƙe ƙarin bayani, ciki har da sunayen gwarzayen da suka rasu, har zuwa bayan sa’o’i 24 bayan an sanar da ‘yan ‘yanuwansu ,” in ji hedikwatar tsaron..

Shugaba Donald Trump ya bayyana mace-macen a matsayin “abun matuƙar baƙin ciki .”

TRT

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *