KANO: GWAMNATI TA DAKATAR DA DURBAR DA HAWAN DAWAKAI A BIRNI SABODA DALILAN TSARO

IMG 173635 27926 1790527002796

KANO:

Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da dukkan nau’o’in jerin gwanon Durbar da hawan dawakai a cikin birnin Kano, har sai baba ta gani.

 

Gwamnatin ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan wani taron gaggawa na Majalisar Tsaro ta Jihar da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Jihar Kano, inda aka duba yanayin tsaro da ya shafi shirye-shiryen gudanar da ayyukan.

 

A cikin sanarwar da Darakta-Janar mai kula da Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi, gwamnatin ta ce matakin na daga cikin matakan kariya da aka ɗauka domin hana yiwuwar arangama, kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da zaman lafiya da doka da oda.

 

Gwamnatin ta ce bayanan tsaro sun nuna cewa an samu gagarumin gangamin magoya baya dangane da shirye-shiryen ayyukan, lamarin da ya haifar da fargabar yiwuwar samun rikici da kuma tabarbarewar doka da oda.

 

Saboda haka, Majalisar Tsaro ta Jihar ta bayar da umarnin dakatar da jerin gwanon Durbar da hawan dawakai da aka shirya gudanarwa.

 

Haka kuma, an umurci dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa da su tabbatar da aiwatar da umarnin, tare da ɗaukar matakin da doka ta tanada kan duk wanda ya karya umarnin ko kuma ya aikata wani abu da ka iya barazana ga zaman lafiya da tsaron jama’a.

 

Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga mazauna jihar, hukumomin gargajiya, ’yan siyasa, magoya bayansu da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankula, su kasance masu bin doka da oda, tare da cikakken bin wannan umarni.

 

Gwamnatin ta kuma tabbatar wa al’ummar Kano cewa tana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da zaman lafiya da doka da oda a faɗin jihar.

 

📢 KU CI GABA DA BIN ALFIJIR LABARAI

 

Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sabbin labarai, rahotanni, bincike, shirye-shirye da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

 

📞 TUNTUBE MU

 

Domin samun ƙarin bayani, turo mana da labari, haɗin gwiwa, tallace-tallace, ɗaukar nauyin shirye-shirye ko wasu buƙatu:

 

📱 +234 803 207 7835

 

📰 Kuna da labari ko wani muhimmin bayani?

Ku turo mana da labaran gaggawa, sanarwar hukumomi, jawabi, sanarwar taro da abubuwan da suka shafi al’umma domin tantancewa da yaɗawa.

 

🤝 KU YI HAƊIN GWIWA DA MU

 

Muna maraba da mutane, ƙungiyoyi, hukumomi da ‘yan kasuwa masu sha’awar:

 

• Haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai

• Tallace-tallace

• Daukar nauyin shirye-shirye

• Haɗin gwiwar kamfanoni da hukumomi

• Rahotanni na musamman da bincike

• Tallata taruka da shirye-shirye

 

📞 Domin tattaunawa:

+234 803 207 7835

 

🌐 KU BI MU A KAFAFEN SADA ZUMUNTA

 

🐦 X (Twitter):

 

“Ku bi mu a X” https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

📘 Facebook:

 

“Ku bi mu a Facebook” https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

🧵 Threads:

 

“Ku bi mu a Threads” https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

▶️ YouTube:

 

“Ku yi Subscibe a YouTube https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

📸 Instagram:

 

“Ku bi mu a Instagram” https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

📲 SHIGA GROUP WHATSAPP

 

Ku kasance cikin masu samun sabbin labarai, shirye-shirye, rahotanni da muhimman sanarwa kai tsaye ta WhatsApp.

 

👇👇

https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f?s=cl&p=a&mlu=4&ilr=4

 

ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES

 

Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce

 

📰 Labarai • Rahotanni • Bincike • Shirye-shirye • Wayar da Kai

 

© 2026 Alfijir Labarai Media Services

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *