Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Amaryar da ta Kashe Mijinta Kwanaki Tara da Aurensu A kano

FB IMG 1760790928482

Babbar Kotun Jihar Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Maryam Ahmed Sabo, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Saudat Jibrin Farawa bayan ta same ta da laifin daba wa mijinta wuka ya mutu har lahira, kwanaki tara kacal da daura aurensu.

A cewar takardar tuhuma da aka gabatar, Saudat Jibrin mai shekaru 19, mazauniyar unguwar Farawa a cikin birnin Kano, ta aikata laifin ne a ranar 9 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 9 na dare.

An tuhume ta da laifin kisan kai bayan ta yanka wuyan mijinta, Salisu Idris, da wuka bayan ta ba shi abin sha na sobo, wanda hakan ya jawo mutuwarsa.

Laifin ya sabawa Sashe na 221 (A) na Dokar Final Kod.

A ranar 20 ga Yuni, 2025, aka gurfanar da ita a gaban Mai Shari’a Maryam Sabo, inda ta ce ba ta aikata laifin ba.

Lauyan gwamnati, Barrister Lamido Abba Soron Dinki, ya kira shaidu biyu: ASP Ezekiel wanda ya rubuta bayanin amincewar laifin a ofishin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda ta Kano, da mahaifin mamacin, Alhaji Idris Danlarai.

Haka kuma, Barrister Soron Dinki ya gabatar da hujjoji guda biyu: bayanin amincewar laifin da wukar da aka yi amfani da ita wajen aikata laifin.

A gefe guda, Lauyan kariya, Barrister Abdulfatah Muhammad, ya gabatar da Saudat Jibrin a matsayin shaida guda daya, don kare kanta.

Shaida na farko, ASP Ezekiel, ya shaida wa kotu cewa ya karbi rahoton kisan kai daga ofishin Yansanda na Mariri, sannan ya je wurin da aka aikata laifin don gane wa idanunsa, inda ya dauki rubutaccen bayanin amincewar laifin a Hausa a wurin Saudat, daga baya ya fassara shi zuwa Turanci.

Karanta Labari: Kotu ta yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi satar wayar Samsung da kuma kisan kai

Shaida na biyu, Idris Danlarai, mahaifin mamacin, ya shaida cewa auren dansa bai wuce kwanaki tara ba.

Ya ce gidansa yana kusa da na dansa, kuma bayan ya samu labarin abin da ke faruwa, ya yi kokarin shiga, amma sai ya tarar an kulle daga.

Daga baya a cewarsa ya haura ta bayan gidan inda ya shiga.

Ya ce ko da shigarsa sai ya tarar da dansa kwance cikin jini da wuka a wuyansa, sannan ya garzaya da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH).

A hanya, dansa ya shaida masa cewa matarsa Saudat ce ta daba masa wuka. Sai dai kafin su isa kofar asibitin AKTH, ya rasu.

Da take kare kanta, Saudat ta musanta aikata laifin, ta ce sa hannun da ke cikin bayanin amincewar laifin ba nata ba ne.

Ta shaida cewa a ranar, mijinta ya dawo gida da halayya mai ban mamaki, sannan ta shiga bandaki.

A cewarta, wasu da ba a sani ba ne suka kashe mijinta yayin da ita ke cikin bandaki.

Lauyan dake kareta ya gabatar da hujjoji hudu don tantance shari’ar, ciki har da cewa babu rahoton likita ko shaidar ido.

Sai dai Lauyan gwamnati ya ce hujjojin da ya gabatar sun hada da bayanin amincewar laifin, bayanin mamacin kafin rasuwa, da sauran hujjoji masu karfi.

Mai Shari’a Maryam Ahmed Sabo ta ce bayan nazarin hujjoji da shaidu, ta yanke hukunci cewa an tabbatar da laifin.

Ta bayyana cewa hujjojin da aka gabatar sun isa don tabbatar da kisan kai ba tare da rahoton likita ba.

Ta ce hujjojin sun nuna cewa Saudat ita ce ta kashe mijinta, kuma babu wata shakka a kokwanto cikin shaidar da lauyan Gwamnati ya gabatar.

Mai Shari’a Sabo ta ce: “Kotu ta same ki da laifin kashe mijinki bayan kwanaki tara da aure. Kotu ta yanke miki hukuncin kisa ta hanyar rataya, ko ta kowace hanya da doka ta tanada. Hukuncin na iya kasancewa bisa yardar Gwamna.”

Kotun ta kuma shawarci hukumomin tsaro da su rungumi hanyoyin bincike na zamani don taimaka wa kotuna wajen shari’o’in kisan kai.

Bayan yanke hukuncin, Saudat cikin fushi ta fada wa Lauyan Gwamnati cewar “Hukuncin kotu ba hukuncin Allah ba ne.”

Da yake zantawa da Justice Watch Hausa bayan zaman kotun, Lauyan gwamnati, Barrista Soron Dinki, ya ce halayyar Saudat a lokacin shari’a ba ta nuna nadama ba.

Ya yaba wa Mai Shari’a Maryam Sabo bisa yanke hukunci da ta yi bisa adalci ga yan uwan mamacin.

A nasa bangaren, Lauyan kariya, Barrister Abdulfatah Muhammad, ya ce ya gano wasu kura-kurai don haka a cewarsa zai yi nazari kan hukuncin sannan ya yi la’akari da yiwuwar daukaka kara a Kotun Daukaka Kara.

Justice Watch

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *