Daga Aisha Salisu Ishaq
Rundunar โyan sandan jihar Kano ta samu gagarumar nasara wajen yaki da miyagun laifuka, inda ta kama wasu da ake zargi da aikata manyan laifuka da dama.
Kwamishinan โyan sandan jihar, CP Salman Dogo Garba ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar โyan sandan Bompai Kano.
Ya ce rundunar ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da kuma kashe Alhaji Atiku Muโazu, mai shekaru 64 da haihuwa mazaunin Janbulo, Kano.
Wadanda ake zargin, Abubakar Hassan (wanda aka fi sani da Captain), Adamu Abubakar Adam, da Alhaji Hamisu (wanda aka fi sani da Bakin Bross), an kama su ne bayan wani ci gaba da bincike da jamiโan leken asiri suka yi.
A wani labarin kuma wasu โyan bindiga sun kai farmaki gidan Alhaji Auwalu da ke Sabuwar Unguwa Garo a karamar hukumar Kabo a Kano, inda suka yi masa fashin Naira miliyan 8 tare da yin garkuwa da โyarsa Zainab Aliyu mai shekaru 16.
CP Salman Dogo Garba ya ci gaba da cewa, โyan sanda sun fara gudanar da bincike domin ceto wanda aka kashe tare da damke wadanda suka aikata laifin.
Kwamishinan โyan sandan ya ci gaba da bayyana cewa, a wani samame na daban, rundunar โyan sandan ta kama wasu mutane 17 da ake zargin โyan fashi da makami ne da suka abkawa Hotoro a Kawo Kano, inda suka farfasa shaguna da motoci, tare da far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
โAn kuma kama wasu mutane uku da ake zargin โyan fashi da makami ne da laifin kai hari ga wasu mutane biyu da ba su ji ba ba su gani ba, tare da yi musu fashin wayoyin hannu guda 200 a unguwar Yankatsari da ke Kano.
CP Salman Dogo Garba ya bukaci jamaโa da su kiyaye da taka tsantsan, kuma su kai rahoto ga ofishin โyan sanda mafi kusa da su ko kuma ta lambobin hukumar: 08032419754, 08123821575, 09029292926.











Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan ๐
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ๐๐
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ
