Binciken bayanan kashe kudaden gwamnati ya nuna cewa Fadar Shugaban Kasa ta kashe Naira biliyan 37.64 kan tafiye-tafiyen cikin gida da na kasashen waje, tare da wasu kudaden da suka shafi tafiye-tafiye daga watan Yunin 2023 zuwa Afrilun 2026. Bayanai daga GovSpend sun nuna cewa kudin sun hada da tafiye-tafiyen shugaban kasa da kuma kudin gudanarwa.
Bayanan sun kuma nuna cewa tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje sau 51, inda ya shafe kusan kwanaki 261 a wajen Najeriya. Tafiye-tafiyen sun kai shi zuwa kasashe akalla 30, yayin da hutunsa na makonni uku a Turai ya kara yawan tafiye-tafiyensa zuwa sau 52.
A cewar bayanan GovSpend, an kashe Naira biliyan 9.18 a rabin shekarar 2023, Naira biliyan 25.26 a shekarar 2024, da Naira biliyan 2.70 a shekarar 2025. Daga watan Janairu zuwa Afrilun 2026 kuma, Fadar Shugaban Kasa ta kashe sama da Naira miliyan 477 kan tafiye-tafiye da sauran abubuwan da suka shafe su.
A gefe guda, bayanan sun nuna cewa an ware dalar Amurka 553,884 domin tafiye-tafiyen Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu, tsakanin 2023 da 2024, wanda darajarsa ta kai Naira miliyan 700.7. Sai dai shugaban Transparency and Accountability Group, Ayo Ologun, ya bukaci a binciki tushen kudaden da kuma sahihancin doka wajen kashe kudin.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
