Rundunar yan sandan jihar Kano ta ceto wani yaro mai shekaru tara, mai suna Ubaiyu Muhammad Sammani, da aka sace a unguwar Rimin Kebbe, tare da cafke mutane 10 da ake zargi da hannu kan lamarin.
Kakakin rundunar yan sandan Kano, rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an sace yaron ne a ranar 6 ga Yuli, 2026, inda masu garkuwar suka nemi a biya su dala dubu 30,000 a matsayin kudin fansa kafin sakin sa.
Ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane suka fara gudanar da bincike ta hanyar amfani da bayanan sirri da kuma hadin gwiwar al’umma, wanda ya kai ga kama mutane 10, ciki har da mace guda.
Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun taka rawa wajen boye yaron da neman kudin fansa, da kuma sauya wurin da ake tsare da shi.
Rundunar ta kuma bayyana cewa wanda ake zargi na farko, Abubakar Salihu, wanda aka fi sani da Sankolo, ya tsere, kuma ana ci gaba da neman sa.
An ceto yaron ne da safiyar ranar 31 ga Yuli a yankin Karshen Kwata da ke Rimin Kebbe a Karamar Hukumar Ungogo.

Daga bisani aka garzaya da shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda likitoci suka tabbatar da lafiyarsa.
Kwamishinan yan sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da kokarin jami’an da suka gudanar da aikin, tare da jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace domin dakile garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a fadin jihar.
Tsaro Da Shari’a
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
