Kungiyar ‘Yan Jaridu Ta Yanar Gizo Ta Horar  Da Mambobinta Kan Ɗaukar Rahoton Zabe A Kano

IMG 212250 29726 1785356592543

Kungiyar ’Yan Jaridar Yanar Gizo a Kano, tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Aminu Magashi Garba, ta shirya taron horaswa na yini guda domin ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida wajen bayar da rahotannin zaɓe da kuma kare lafiyarsu yayin gudanar da ayyuka gabanin zaɓen 2027.

Taron ya gudana a yau Laraba, 29 ga Yuli, 2026, a Sakatariyar ’Yan Jarida da ke Farm Center cikin birnin Kano.

Taron ya haɗa ’yan jarida daga kafafen yaɗa labarai na yanar gizo, inda aka koyar da ɗabi’un aikin jarida, tantance sahihan bayanai, yadda za a ɗauki rahoton zaɓe da kuma matakan kare kai yayin rikice-rikice a zaɓe.

Da yake jawabi yayin gabatar da maƙala a wajen taron, Comrade Abbas Ibrahim tsohon shugaban ƴan jarida ta Kano ya jaddada muhimmancin sahihanci, adalci da rashin nuna son kai wajen rahoton zaɓe, tare da kira ga ’yan jarida da su guji yaɗa bayanan ƙarya.

A nasa bangaren kuwa, Isyaku Ahmad ya bayyana muhimmancin bin ƙa’idojin aikin jarida yayin ɗaukar rahoton zaɓe, tare da bayyana dabarun fuskantar ƙalubalen da ka iya tasowa.

Taron dai ya zo ne yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *